
Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdurahmane Tchiani ya bayar da umarnin tura tankoki 100 shaƙe da man fetur zuwa Mali domin taimaka wa mahukuntan wannan ƙasar da ke cikin ƙawancensu na AES magance matsalar ƙarancin man da ta ke fuskanta a ƴan kwanakin nan.
Tun bayan da mayaƙan JNIM dake iƙirarin jihadi suka sanar da dakatar da shigar da mai ƙasar ta yammacin Afrika, al’amura suka tsaya cak.
- Jamhuriyar Nijar ta yi Karin albashin ma’aikata zuwa N108,000
- Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kwace wuraren hakar Zinare daga kamfanin kasar Australia.
A halin yanzu ma gwamnatin sojin ta dakatar da ƙanana da manyan makarantu a faɗin ƙasar na tsawon makonni biyu saboda ƙarancin man da ake fuskanta.
Baya ga tsayar da al’amura cak a Malin da mayaƙan suka tilasta yi, sun kuma zafafa kai hare-hare, inda suka ƙwace iko da ƙauyuka da dama.




