DuniyaLabaraiSiyasa

Za mu tabbatar mun dawo da doka da oda a Kamaru – Paul Biya

Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi alƙawarin dawo da doka a ƙasar bayan tashin hankalin da aka samu bayan zabe.

Mista Biya mai shekara 92 wanda ya kama aiki a karo na takwas, ya ɗaura alhakin tashin tashinar kan abin da ya kira yansiyasa “marasa hankali”.

Bayyana Mista Biya a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ta tunzura gudanar da zanga-zanga mai muni da nuna tirjiya, wadda ta kai ga mutuwar masu zanga-zangar.

Sai dai a jawabinsa na kama aiki, shugaban ya jinjina wa jami’an tsaron kasar.

Bayan shekara 43 yana mulki, shugaban ya sake nanata aniyarsa ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi mata da matasa, tare da alkawarin kawo ƙarshen cin hanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Prove your humanity: 9   +   10   =  

Back to top button