AfrikaDuniyaLabarai

Rikici ya barke tsakanin Kungiyan Boko Haram da ISWAP 

Rikici ya barke tsakanin Kungiyan Boko Haram da ISWAP

Bangarorin sun ci gaba da gumurzun hamayya a tsaƙaninsu a yankin Tafkin Chadi na jihar Barno, makonni biyu bayan ƙoƙorin sulhunta bangarorin biyun ya ci tura.

Rahotanni na cewa, wannan ba shine karon farko da bangaren Boko Haram da Bakura Doro ke jagoranci ke fafatawa da Iswap ba a karamar hukumar Abadam dake tafkin Chadi.

A cewar masanin kan harkokin da suka shafi ta’addanci Zagazola Makama, fafatawar bangarorin biyu na baya-bayan nan ya wakana ranar Jumma’ar da ta gabata a wani sansanin mayakan ISWAP dake Toumbun Gini da Toumbun Ali.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Makama ya ce akwai yiwuwar gurmuzun ya faɗaɗa zuwa ƙaramar hukumar Kukawa inda bangaren Boko Haram suka yi kaka gida saboda illar da suka yi wa ISWAP a faɗar ta baya-bayan nan a kan ruwa.

Kungiyoyin biyu na rikici da juna tun bayan da ISWAP ta ɓalle daga cikin Boko Haram tare da mubaya’a ga ƙungiyar IS a shekarar 2016.

Mayakan ISWAP sun kashe tarin sojojin Najeriya a wani farmaki,Yan ta’adda da dama sun mutu a fadan tsakanin Boko Haram da ISWAP.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Prove your humanity: 0   +   3   =  

Back to top button