
- An kubutar da mutane 59 a jihar kaduna
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu ya mikawa gwamnatin jihar Kaduna mutane 59 da aka kuɓutar daga hannun masu garkuwa da mutane.
Mutanen da aka kuɓutar sun hada da maza da mata da kananan yara shida, jami’an tsaro ne suka ceto su a wani hari da suka kai wa ‘yan bindigar.
Wadanda aka kuɓutar, sun shafe fiye da watanni hudu a sansanin masu garkuwa da mutane.
Ribadu ya bada tabbacin cewa, jami’an tsaro za su ci gaba da ceto duk mutanen da aka yi garkuwa da su tare da kawar da duk wata barazanar ‘yan ta’adda a fadin kasar nan.
#Leadership



