
Shugaban Ƙasar Amurka, Donald J. Trump, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan abin da ya kira “barazana ga rayuwar Kiristoci” a Nijeriya, bayan rahotannin da ke nuna cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, Trump ya zargi ƙungiyoyin ‘yan ta’adda masu iƙirarin ɗaukaka addinin Musulunci da kasancewa silar wannan tashin hankali, tare da kiran gwamnatin Amurka da ta ɗauki mataki cikin gaggawa.

Ya bayyana cewa ya sanya Nijeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Barazana” saboda yawan kashe-kashen da ake yi, inda ya ce daga cikin Kiristoci 4,476 da aka kashe a duniya, 3,100 na daga Nijeriya suke.
Trump ya ƙaƙaba sabon haraji kashi 100 kan kayayyaki daga ƙasashen waje
“Dole ne a ɗauki mataki kan irin kisan da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya,” in ji Trump.
Ya roƙi ɗan majalisar Amurka Riley Moore, shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisa Tom Cole, da sauran ‘yan majalisar su binciki lamarin tare sa kai masa rahoto.




