Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na da ‘yancin tsayawa takarar shugabancin ƙasar a shekarar 2027.
Sai dai ta jaddada cewa ‘yan Najeriya ne za su yi masa hukunci saboda ba za su manta ‘munin’ mulkin Jonathan ba, ta kuma kwatanta mulkin Tinubu da abin da ta bayyana a matsayin “gagarumin ci gaban tattalin arziƙi”
Fadar shugaban ƙasar ta kuma ɗora alhakin fara yaƙin neman zaɓe da wuri kan masu neman kifar da shugaba mai ci.
Hakan na zuwa ne a rana guda da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ba za ta bai wa Jonathan tikitin tsayawa takara kai tsaye ba, inda ta bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin “zaɓuɓɓukan da take dubawa.