DuniyaLabarai

Trump ya ƙaƙaba sabon haraji kashi 100 kan kayayyaki daga ƙasashen waje

Gwamnatin Amurka ta sanar da sabbin haraji kan kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga ƙasashen waje.

Shugaba Trump ya ce daga ranar Laraba, kamfanonin samar da magunguna da ke shigar da su kasar za su fuskanci harajin kashi 100 cikin 100 matsawar basu fara samar da masana’antunsu ba Amurka.

Manazarta sun yi imanin cewa harajin zai cutar da ƙasashe irin su Ireland, wacce ta fi kowace kasa fitar da magunguna zuwa Amurka.

Trump ya kuma ba da sanarwar ƙarin haraji kan kayayyaki daban-daban tun daga manyan manyan motoci zuwa kayan kicin da na daki da sauransu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Prove your humanity: 2   +   1   =  

Back to top button