“Ana nuna wa mata wariya a harkar ƙwallon ƙafa” Mai horda da Chelsea

0
51

Mai horad da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta mata Sonia Bompastor ta ce daya daga cikin tambayoyin da ake yawan yi mata wajen tantancewar daukar aiki ita ce ko za ta iya jagorantar babbar kungiya kuma tana mace uwa.

Bompastor, wadda take da ‘ya’ya hudu ta jagoranci Chelsea ta ci kofi uku a Ingila a baya.

Da aka tambaye ta game da wani bincike da aka yi kwanan nan wanda ya gano cewa kashi 78 cikin dari na mata na fuskantar wariya a harkar wasan kwallon kafa, sai ta ce ba ta mamaki.

”Ka san tambayar farko da kowa yake yi min idan ina neman aikin kociya,” in ji Bompastor mai shekara 45.

“Zan gaya maka – ‘kina ganin abu ne da zai yiwu ki kisance uwa mai ‘ya’ya hudu kuma mai horad da wata babbar kungiya?’

“Ina ganin idan namiji ne a gabansu suke tantancewa ba za su taba yi masa wannan tambayar ba.”

Amma kuma tana dariya ta kara da cewa: “Ba haka lamarin yake a Chelsea ba.”

Binciken wanda aka bayyana ranar Laraba ya nuna cewa wariyar da ake nuna wa mata a harkar wasan kwallon kafa na da yawa kuma ana yi sosai.

Ya gano cewa kashi 63 da rabi na mata da ke aiki a bangaren wasan kwallon kafa na fuskantar shagube ko barkwanci na lalata, yayin da kashi 56 cikin dari suka ce ba a daukar wani mataki a kan yi musu hakan, bayan sun kai rahoto na wariyar a wurin aiki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 5   +   3   =