Siyasa

Ana tuhumar tsohon Firaministan Mali da wawushe duƙiyar al’umma

 

Masu gabatar da ƙara a Mali na tuhumar tsohon Firaministan ƙasar, Choguel Kokalla Maiga, da wawushe duƙiyar al’umma.

Mista Maiga na tsare a gidan yari zuwa lokacin kammala yi masa shari’a.

Akwai kuma tsoffin abokan aikinsa tara da su ma suka gurfana a gaban kotun koli, inda aka gabatar da tuhuma kan mutum biyu, wasu kuma an wanke su.

A makon da ya gabata aka kama Mista Maiga, kwanaki bayan gwamnatin soji ta kama gwamman mutane da ake zargi da yunkurin juyin-mulki a cikin sojoji.

A watan Nuwamba aka soke shi daga mukaminsa bayan ya soki lokacin da aka tsara na mayar da mulki hannun farar-hula.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Prove your humanity: 1   +   2   =  

Back to top button