
Kaftin kungiyar Real Madrid kuma dan Asalin kasar Croatia Luka Modrić yayi bankwana da magoya bayan kungiyar bayan sun sami nasara akan kungiyar Real Sociedad da ci 2 da nema.
Haka zalika shima abokin ƙungiyar tasa kuma dan asalin kasar andlus lucas Vasquez shima yayi bankwana da magoya bayan.
Saidai Luka modrić yayi ƙoƙarin zama a ƙungiyar amma ita ƙungiyar ta ki amincewa dan bukatar sa.
Dan wasan dai ya taka rawar gani a ƙungiyar ya lashe kofina 28 tare da real Madrid wanda ya hada da kofin nahiyar turai guda 6 , kofin gasar laliga kuda 4 ga kuma Copa del Rey 2.
Dan wasan dai zai bar kungiyar bayan ya buga final din FIFA CLUB WORLD CUP na shekarar 2025.




