An hana Shugaban Yan’adawa na Ivory Coast Takara
Shugaban ‘yan adawa na Ivory Coast ba zaiyi takara ba.Kotu a Ivory Coast ta haramta wa madugun ‘yan adawa yin takaraKotu a Côte d’Ivoire ta haramta wa madugun ‘yan adawar ƙasar, Tidjane Thiam, tsayawa takarar shugabancin ƙasar, yayin da watanni shida suka rage a gudanar da zabe, da shiga al’amuran siyasa gabadaya kamar yadda guda daga cikin lauyoyinsa ya tabbatar.
Kotun ta ce an yanke hukuncin haramta masa tsayawa takarar ne, saboda ya rasa damar kasancewa ɗan ƙasar ta Ivory Coast.
Hukuncin kotun wanda babu damar daukaka shi, ya kawo ƙarshen mafarkin Tidjane na fafatawa a babban zaɓen wannan ƙasa da za a yi a rana 25 ga watan Oktoban wannan shekarar.Ayayin zaman sauraron bahasin, alƙalin kotun ta ce, madugun ‘yan adawar ya rasa damar kasancewa dan kasar ne, saboda yana amfani da takardun shaidar dan kasar Faransa, kan haka ne ta amince da bukatar da masu shigar da kara suka gabatar mata, na janye sunan Tidjane Thiam din daga cikin jerin wadanda suka tsaya takarar shugabancin kasar.
An haifi Tidjane Thiam a ranar 29 ga watan Yulin shekarar 1962, a birnin Abidjan kuam yana ɗauke da ruwa biyu ne, la’akari da cewar mahaifansa sun fito ne daga Senegal da kuma Cote D’Ivoire, kuma guda ne daga cikin manyan ƴan kasuwar da ƙasar ke ji da su.
Mahaifinsa Amadou Thiam ɗan jarida ne daga ƙasar Senegal ya kuma dawo ƙasar ta Cote d’Ivoire a shekarar 1947, kuma magoyin baya ne ga Houphouet-Boigny, yayinda yake yaƙin kwatar yancin ƙasar.
A shekarar 1984 shi kaɗai ne wanda ya sami nasarar shiga kwalejin koyarda harkokin siyasa ta birnin Paris wadda ya kammala a shekarar 1986.
Thiam ya fara shiga harkokin siyasa a shekarar 1998 inda ya zama shugaban ƙaramar hukuma, kafin daga bisani a naɗa shi ministan tsara birane da cigaba na ƙasar.




