Matatar Dangote ta dawo da siyar da fetur da Naira, ƙasa da sa’o’i 24 da dakatar da tsarin
Matatar ta dauki wannan matakin biyo bayan tsoma baki da shugaban kwamitin sayar da danyen mai da Naira ga matatun cikin gida, Dr. Zacch Adedeji, wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar Kula da Haraji ta Ƙasa (FIRS).
Tsarin “Naira for Crude” wanda gwamnatin tarayya ta kafa ta hannun NNPCL yana bai wa matatun cikin gida damar samun danyen mai ta hanyar biyan kuɗi da Naira, domin rage dogaro da dala da kuma tabbatar da wadatar mai a ƙasar.