Raunin Camavinga ya rage darajar kasuwarsa a Real Madrid

0
54

Dan wasan tsakiyar Real Madrid, Eduardo Camavinga, na fuskantar koma baya a darajar kasuwarsa bayan jerin raunuka da suka takaita damar buga wasa a shekarar da ta gabata.

A cewar shafin Transfermarkt, darajar Camavinga ta ragu daga Yuro miliyan 100 a watan Yunin 2024 zuwa Yuro miliyan 50 a halin yanzu — raguwa mai nisan gaske da ke nuna yadda rashin samun damar taka leda ya shafi cigaban aikinsa.

Dan wasan mai shekaru 22 ya yi fama da rauni da kuma rashin samun isasshen lokaci a cikin manyan wasanni, lamarin da ya hana shi fitowa akai-akai a jerin ‘yan wasa na farko a Real Madrid.

Tun bayan dawowarsa daga raunin da ya samu kwanaki 19 da suka gabata, Camavinga ya buga mintuna 76 kacal a wasa daya, abin da ya nuna cewa koci Carlo Ancelotti na ci gaba da kula da lafiyarsa kafin ya dawo cikin cikakken ƙarfi.

Farawar sa ta ƙarshe a gasar La Liga ta kasance a ranar 20 ga Afrilu, 2024, a wasan da Real Madrid ta fafata da Athletic Bilbao, kafin ya sake samun ciwon tsoka a kakar 2023-24 wanda ya jefa shi cikin jinkirin dawowa.

Masu sharhi a fannin kwallon kafa sun bayyana cewa Camavinga na da gagarumin buri da baiwa, kuma da zarar ya murmure gaba ɗaya daga raunuka, zai iya dawo da martabar sa a matsayin ɗaya daga cikin matasan ‘yan wasa mafiya ƙarfi a Turai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   2   =