LabaraiSiyasa

Akpabio na azabtar da ni ne saboda na ƙi yarda ya kwanta da ni – Sanata Natasha

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP, Kogi ta Tsakiya) ta zargi shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da neman saduwa da ita.

‘Yar majalisar wacce labarin ta ya mamaye kafafen yada labarai bisa rikicin ta da shugaban majalisar Dattawa, ta yi wannan ikirarin ne a gidan talabijin na ARISE, a yau Juma’a.

A hirar da ta yi da manema labarai a ranar Juma’a, ‘yar majalisar ta ce tana da shaidu a kan Akpabio, inda ta bayyana cewa mijinta ma shaida ne.

Ta ce tana da bayanai da ta bugo a rubuce kuma ta kalubalanci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta fitar da cikakkun bayanai na tattaunawar ta da akpabio inda ta ce “saboda kullum yana kirana a WhatsApp.”

 

Ta ce: “Rigimar ta da Akpabio ta samo asali ne tun a ranar 8 ga Disamba, 2023 lokacin da ni da mijina mu ka ziyarci Akwa Ibom domin bikin zagayowar ranar haihuwar Sanata Akpabio. Akpabio ya rike hannu na ya rika nuna min yadda gidan sa ya ke. Ga miji na na biye da mu a baya, ya ce, yana so in zo in yi kwana a gidan a gidan nasa.

“Mijina ya ji shi, daga baya ya ce da ni kada in yi tafiya zuwa kasar waje ni kadai ko in kasance tare da Shugaban Majalisar Dattawa ni kadai.

“Shine daga baya na je na same shi a ofishin sa akan wani ƙudiri na aikin Ajaokuta. Kawai sai ya nuna min wai sai na shakata da shi, na saka shi farin ciki da jin dadi. Shine kawai na fice daga ofishin sa,”cewar Natasha.

“Ni dai yanzu al’amari na da Akpabio ya zama kamar malamin da ke azabtar da daliba saboda ta ƙi yarda ya kwanta da ni,”cewar Natasha.

DAILY TRUST ta ce ta tuntubi mai taimaka wa Akpabio kan harkokin yada labarai, Jackson Udom, amma bai amsa kiraye-kirayen waya da ta yi masa ba a safiyar yau Juma’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Prove your humanity: 7   +   6   =  

Back to top button