Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Namadi Sambo, murna bisa nadin sa a matsayin Sardaunan Zazzau, wanda Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya nada shi a Zariya, Jihar Kaduna, a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025.
A wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban ƙasa, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa wannan nadin mukami na Sardaunan Zazzau yana da matuƙar daraja a tsarin al’adu da tarihin Arewacin Najeriya. Ya ce wannan girmamawa alama ce ta yadda masarautar Zazzau ta yaba da basira, nagarta, da jajircewar Namadi Sambo wajen bayar da gudummawa ga ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya.
Shugaban ƙasa ya kara da cewa nadin ya dace da irin rawar da Sambo ya taka a fannoni daban-daban na gwamnati da al’umma, musamman a lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa, inda ya yi aiki tukuru wajen bunƙasa ci gaban ƙasa da haɗin kan ‘yan Najeriya.
Tinubu ya kuma yabawa Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, bisa ci gaba da riƙe da al’adun girmamawa ga mutanen da suka yi fice wajen shugabanci, kishin ƙasa da kuma ƙarfafa zaman lafiya a cikin masarautar da ma ƙasar baki ɗaya.
Shugaban ƙasa ya yi fatan Allah Ya ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo, nasara da ƙarfin guiwa a wannan sabuwar rawar da zai taka. Ya kuma bukace shi da ya ci gaba da zama abin koyi ga matasa, tare da yin aiki tare da shugabannin gargajiya domin ƙara haɓaka zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban al’umma.