Kotun Shari’ar Musulunci da ke Garun Malam ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Malam Naziru Abdullahi Tamburawa ta fara sauraron shari’ar wasu mutane shida da ake zargi da hannu a satar wata tinkiya mai kimanin naira dubu saba’in (₦70,000).
Rahotanni daga Arewa Updates sun bayyana cewa lamarin ya samo asali ne daga wani magidanci da ke ƙaramar hukumar Kura, wanda ya sayi tinkiya a kasuwar Kura domin yin haƙiƙa idan matarsa ta haihu. Sai dai wani maƙwabcinsa Bafulatani ya zargi cewa tinkiyar da aka saya tasa ce da ta ɓace, lamarin da ya kai ga kai ƙara ofishin ‘yan sandan Kura.
Binciken da rundunar ‘yan sanda ta gudanar ya gano wasu dillalan da suka shiga cikin cinikin tinkiyar, ciki har da wanda ya kawo dabbobin kasuwa da kuma wanda ya saya. Daga bisani an gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar shari’a.
Mai gabatar da ƙara, Insfekta Nasiru Abubakar Dan Sakkwato, ya karanta musu takardar tuhuma a gaban kotu, yayin da Alkalin ya umarci a kawo tinkiyar domin tabbatar da ita da idonsa. Ya kuma tambayi Bafulatanin wanda yake ikirarin mallaka ko yana da shaidu ko hujjoji da ke tabbatar da tinkiyar tasa ce.
Bayan sauraron bayanan ɓangarorin, kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Oktoba, 2025, tare da bayar da umarni ga jami’an tsaro da su kawo mutumin da ya ce ya siyo tinkiyar a kasuwar Gwaram, Jihar Jigawa, domin ci gaba da bincike da tabbatar da gaskiya.
Wannan shari’a ta jawo hankalin jama’a a yankin, inda wasu ke ganin cewa irin wannan matsala na nuna bukatar tsaurara matakan tabbatar da gaskiya a harkar kasuwancin dabbobi, musamman tsakanin manoma da makiyaya.