Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihar Kebbi ta kama lita 35,725 na man fetur da wasu kayan fasa kwauri da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 109 a wani sabon samame da ta kaddamar a kan iyakokin jihar.
Kwamandan hukumar a shiyyar Kebbi, Comptroller Mahmoud Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na farko da ya gudanar a ofishin hukumar da ke Birnin Kebbi ranar Laraba.
Ya ce an samu nasarar kama kayan ne ta haɗin gwiwa da tawagar Operation Whirlwind, rundunar musamman ta hukumar kwastam da ke yaki da fasa kwauri.
“Tawagar Operation Whirlwind ta kama lita 14,750 na man fetur da kudin su ya kai Naira miliyan 8.85, yayin da jami’an shiyyar Kebbi suka kama wasu lita 20,975 da darajarsu ta kai Naira miliyan 12.58 a wurare daban-daban kamar Bagudo, Tsamiya, Kamba, Lolo, Bunza da Zuru,” in ji Ibrahim.
Ya ce waɗannan kamen sun nuna jajircewar hukumar wajen kare albarkatun ƙasa da kuma tattalin arziƙin ƙasa daga masu lalata tattalin arzikin ƙasa ta hanyar fasa kwauri.
Kwamandan ya yaba da kokarin jami’an da ke filin aiki, sashen leken asirin hukumar da sauran jami’an tsaro bisa haɗin kai da kwazo wajen aiwatar da aikin.
Ya ƙara da cewa man fetur ɗin da aka kama za a sayar bisa ka’idojin doka, inda kuɗaɗen za su shiga baitul-mali na tarayya.
Ibrahim ya kuma bayyana cewa hukumar ta tara harajin sama da Naira miliyan 25.6 a watan Satumba, adadin da ya karu da kaso 36 cikin 100 idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
A cewarsa, wannan ci gaba ya biyo bayan ingantaccen hulɗa da masu ruwa da tsaki, kyautata tsaron iyakoki da kuma haɗin kai da hukumomin tsaro da ke iyakar Nijar ta Kamba.
Ya ƙara da cewa hukumar ta kuma kama buhun kaya 100 na tufafi na second-hand, buhuna 444 na tabar wiwi, katan 140 na taliya, buhuna 100 na shinkafa, da jarkoki 20 na man gyada.
Kwamandan ya ce za a mika tabar wiwin ga hukumar NDLEA, yayin da naman jakin da aka kama za a mika ga hukumar kula da lafiyar kayan abinci da dabbobi ta ƙasa, Nigeria Agricultural Quarantine Service (NAQS).
Ibrahim, wanda ya hau kan mukamin kwamandan shiyyar a watan Satumba, ya sha alwashin ci gaba da haɗin kai da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin hana laifukan kan iyaka da kuma inganta kasuwanci na halal.