Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano a Najeriya wato PCACC, ta ce ta fara gudanar da cikakken bincike kan zargin karkatar da wasu kudade fiye da naira bilyan hudu da tsohuwar gwamnatin jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ta yi.
Shugaban hukumar, Saidu Yahaya ya ce binciken da hukumar tasu ta fara gudanarwa ya biyo bayan wani ƙorafi ne da aka kai musu game da batun kuɗaɗen na naira sama da biliyan huɗu da ake zargin tsohuwar gwamnatin Ganduje ta karkatar
“A taƙaice, muna gudanar da bincike a kan wasu kuɗaɗe da aka ɗauka daga gwamnatin jahar Kano aka je aka saka a cikin Dala Inland Dry Port.” in ji shi
“Wannan kudin ya kai sama da naira biliyan huɗu, kuma an ɗauke su ne a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje.
Yayin da BBC ta nemi jin ta bakin malam Muhammad Garba, tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jahar kuma tashon shugaban ma’aikatan tsohon gwamnan Dr Abdullahi Ganduje game da wannan bincike da aka fara, sai ya ce
“Nasan cewa maganar tana kotu to kuma idan magana tana kotu, ban san irin binciken da za ayi ba,.”
“Da na tuntuɓi mai girma tsohon gwamna, Ganduje,wannan binciken ba wani abu ba ne na damuwa, dama ai an saba ana gudanar da irin wannan bincike a wurare daban-daban.” In ji Muhammad Garba.