Fadar Shugaban Kasa ta karyata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawan Najeriya

0
119

Fadar shugaban kasa ta karyata sabon rahoton Bankin Duniya da ya ce mutane miliyan 139 a Najeriya na fama da talauci, tana mai cewa alkaluman sun kauce wa gaskiyar halin tattalin arzikin ƙasar.

Mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai, Sunday Dare, ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya ce rahoton ya dogara ne kan tsofaffin bayanai da kuma tsarin ƙididdiga na duniya da ba su dace da ainihin yanayin Najeriya ba.

A cewar sa, adadin da Bankin Duniya ta fitar ya samo asali ne daga ƙa’idar “$2.15 a rana”, wanda idan aka juyar da shi zuwa kudin Najeriya, ya kai kusan N100,000 a wata,  abin da ya fi sabon mafi ƙarancin albashi da gwamnati ta amince da shi.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin Tinubu tana ɗaukar matakai na tabbatar da dawowar tattalin arziki da rage radadin talauci ta hanyar shirye-shiryen tallafi da cigaba kamar Renewed Hope Programmes, da kuma Cash Transfer ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.

Bankin Duniya dai a ranar Laraba ta fitar da rahoto inda ta nuna damuwa cewa duk da gyare-gyaren gwamnati, adadin talakawa a Najeriya ya karu zuwa miliyan 139 a 2025, daga miliyan 129 a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   2   =