Dan wasan ƙwallon ƙafa na Togo,ya karya wuya yayin wasa a kasar China

0
66

Dan wasan tsakiyar ƙasar Togo, Samuel Asamoah, ya karye a wuya bayan karo da allon talla na gefen fili yayin wasa a kasar Sin, lamarin da kungiyar ƙwallon ƙafar da ya ke taka leda ta ce da wuya idan bai samu ciwon laka ba.

Asamoah, mai shekaru 31, wanda ke buga kwallo a kungiyar ƙwallon ƙafa ta Guangxi Pingguo na rukuni na biyu a kasar, ya bugu da kai cikin allon talla na LED bayan wani dan wasan abokan hamayya ya tura shi yayin wasan cikin gida da aka buga a ranar Lahadi.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, kulob din Guangxi Pingguo ya bayyana cewa dan wasan yana cikin hadarin samun nakasar kafa (high-level paraplegia) bayan an gano yana da karaya da dama a wuya tare da raunin jijiyoyi masu tsanani.

An bayyana cewa an yi wa Asamoah tiyata kuma yana cikin halin da ya daidaita, yayin da kulob din ya ce za a ci gaba da sanar da jama’a ci gaban murmurewarsa bayan ƙarin gwaje-gwaje.

A yayin wasan, dan wasan tsakiyar Chongqing Tonglianglong, Zhang Zhixiong, ya karɓi katin gargadi saboda tura Asamoah cikin allon talla.

Asamoah ya shafe yawancin aikinsa a ƙasar Belgium kafin ya koma China a shekarar 2024, kuma yana da wasanni shida da ya wakilci ƙasar Togo a matakin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   5   =