Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da sabbin ƙa’idoji da za su shafi masu amfani da na’urorin POS da wakilan harkokin kuɗi a faɗin ƙasar. Wannan mataki na nufin ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗi, rage damfara, da inganta ingancin ayyuka.
A cewar sanarwar, daga ranar 1 ga Afrilu, 2026, duk mai sana’ar POS zai iya yin aiki ne da cibiyar kuɗi guda ɗaya kawai – ko dai banki ɗaya, ko kamfanin hada-hadar kuɗi na zamani kamar Opay, Moniepoint, Palmpay, Kuda da makamantansu. Hakan na nufin ba za a yarda da amfani da POS daga wurare daban-daban a lokaci guda ba.
CBN ta kuma bayyana cewa za a iyakanta adadin kuɗin da za a iya cirewa ta POS zuwa N100,000 ga kowane abokin ciniki a rana, yayin da iyakar hada-hadar kuɗi na rana ga wakilin POS zai kasance N1.2 miliyan.
Haka kuma, duk wata na’urar POS za a yi mata rajista ta hanyar “geo-tagging”, wato a sanya alamar wurin da ake amfani da ita. Na’urar ba za ta yarda da amfani a wani wuri daban ba. Idan aka karya wannan doka, mai laifin na iya fuskantar tara mafi ƙaranci Naira miliyan 5.
Wadannan sabbin ƙa’idoji za su fara aiki ne a sabuwar shekara mai zuwa, don haka ana shawartar masu sana’ar POS su binciki sabbin dokokin tun yanzu don su kasance cikin shiri kafin lokaci ya yi.