Muhammadu Inuwa shi ne Sarkin Kanon da ya maye gurbin Sarki Muhammadu Sanusi wanda ya yi murabus a shekarar 1963.
Sarki Muhammadu Inuwa shi ne sarki na 54 a jerin sarakunan Kano, sannan kuma sarki na 12 a jerin sarakunan Fulani.
An yi masa sarautar Kano lokacin yana riƙe da muƙamin Turakin Kano. Sannan kuma ya yi hakimi a Bichi, da kuma gundumar Minjibiri wacce ta haɗa da Kunya da Kuru kafin zamowarsa sarki.
Sarki Muhammadu Inuwa Abbas bai yi tsawon zamani a kan karagar mulkin Kano ba. Ya yi sarauta ta tsawon wata shida kacal.
Sarkin Kano Muhammadu Inuwa Ya rasu a ranar 8 ga watan Oktoba shekarar 1963.
Allah ya jiƙansa da rahama Amin.