An Kaddamar Da Aikin Gina Rijiyoyi Burtsatse 44 a Tudun Wada

0
97

Hukumar Karamar Tudun Wada a Jihar Kano ta kaddamar da aikin gina rijiyoyi burtsatse guda 44 a mazabu 11, tare da samar da fitilun tituna masu amfani da hasken rana.

Shugabar karamar hukumar, Hajiya Sa’adatu Salisu Yushau, ta ce wannan shiri na daga cikin manufofin gwamnatinta na inganta ababen more rayuwa da samar da muhimman ayyuka ga al’umma.

Ta ce majalisar karamar hukumar za ta ci gaba da mayar da hankali wajen tabbatar da samun tsaftataccen ruwan sha mai inganci a dukkan mazabu.

“Mun kuduri aniyar ganin cewa kowane yanki ya samu ruwa mai inganci da kuma fitilu masu amfani da hasken rana domin tabbatar da walwala da tsaro,” in ji Hajiya Sa’adatu.

Shugabar ta kuma mika godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa bai wa kananan hukumomi dama da goyon baya wajen aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.

A nasa bangaren, Daraktan Mulki da Kuɗi na Karamar Hukumar Tudun Wada, Alhaji Ibrahim D. Haruna Bichi, ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da haɗin kai domin ci gaba da aiwatar da irin waɗannan ayyuka.

A cewar Jami’in yaɗa labarai na karamar hukumar, Salisu Kassim Yakasai, aikin na daga cikin shirye-shiryen tabbatar da kyakkyawan rayuwa ga al’umma.

Alhaji Ibrahim Bichi ya ƙara bayyana cewa daga cikin rijiyoyin burtsatse guda 44 da ake ginawa a mazabu 11, an riga an kammala rijiyoyi guda 34, yayin da sauran ke ci gaba da aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   10   =