Ana sa ran dan wasan Real Madrid Trent Alexander-Arnold zai dawo cikin koshin lafiya nan da makonni biyu, in ji majiyoyi. Dan wasan na Ingila, mai shekara 26, ya ji rauni a kafarsa a wasansa na farko na gasar zakarun Turai da Marseille a watan jiya, inda da farko aka yi tuna nin zai yi jinyar makonni shida zuwa takwas.
A cewar Fabrizio Romano, murmurewar Trent na samun ci gaba sosai, kuma kungiyar na da kwarin gwiwar cewa zai samu bayan hutun kasashen duniya da ke tafe.
Manufar shi ne ya kasance cikin koshin lafiya a lokacin wasan El-Clasico na farko a kakar bana da Barcelona a ranar 26 ga Oktoba.
Dani Carvajal shi ma zaiyi jinyar kusan wata guda saboda rauni, dawowar Alexander-Arnold da wuri zai karawa Real Madrid wani muhimmin ci gaba, wanda zai baiwa kungiyar damar samun sassaucin ra’ayi wajen shiryawa a wasan Clasico da karawar da zasuyi da Juventus a ranar 22 ga Oktoba.