Shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa ya ayyana dokar ta-baci a lardina 10 daga cikin 24 na fadin kasar, yayin da zanga-zangar nuna adawa ga gwamnatinsa ta yi sanadin mutuwar mutum guda.
Kungiyar ‘yan asalin Ecuadors ‘CONAIE’ ce ta kira jerin zanga-zangar tun a karshen watan Satumba domin nuna adawa ga matakin gwamnati na cire tallafin man fetur, wanda ya haddasa tashin farashin galan daga dala 1,80 zuwa zuwa dala 2,80.
Masu zanga-zangar sun rinka toshe hanyoyi tare da yin arangama da jami’an tsaro, lamarin da ya haddasa jikkatar mutane akkala 150, tare da kama darurruwan mutane kamar yadda hukumomin kasar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka sanar.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fidda ta ce dokar za ta kwashe kwanaki 60 tana aiki, sannan shugaba Noboa ya bai wa jami’an tsaro umurnin murkushe duk wanda ya sake yunkurin tada fitina.