Ministan Harkokin Kirkire-Kirkire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya amsa cewa Jami’ar Najeriya, Nsukka (UNN), ba ta taɓa ba shi takardar shaidar kammala digiri ba.
Wannan na zuwa ne bayan rahoton binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar na tsawon shekara biyu, wanda ya bayyana cewa jami’ar UNN ba ta bashi takardar shaidar kammala digirin da ya gabatar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Majalisar Dattawa lokacin tantance shi a matsayin minista ba.
Zargin gabatar da takardar shaidar bogin ya biyo Nnaji tun cikin watan Yulin 2023, lokacin da Shugaba Tinubu ya bayyana shi a cikin jerin farko na ministoci 28 daga jihohi 25 da aka tura wa Majalisar Dattawa domin tantancewa, bayan watanni biyu da kama aiki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Daily Trust ta ruwaito cewa masu suka sun yi zargin cewa Nnaji bai kammala karatunsa na jami’a ba, kuma cewa takardar digiri da ta bautar ƙasa (NYSC) da ya mika wa Shugaba Tinubu da ofisoshin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) da Majalisar Dattawa, duk na bogi ne.
Sai dai kuma a halin yanzu, in ji Daily Trust, Nnaji ya bayyana kansa kan zargin a karon farko, inda ya tabbatar da cewa UNN ba ta taɓa ba shi wata takarda ta kammala karatu ba.
Amincewar ministan na ƙunshe ne a cikin wasu takardun kotu da ya shigar a ƙorafin da ya shigar a kotu.
A korafin da ya shigar a babbar Kotun taraiya karkashin Mai Shari’a Justice Hauwa Yilwa, Nnaji ya nemi a hana jami’ar UNN bata masa bayanan karatun sa.