Chanjin shekar Yan wasan kwallon kafa

0
83

Real Madrid na shirin zawarcin dan wasan tsakiyar Manchester City Rodri dan kasar Sipaniya kuma a shirye take ta biya fam miliyan 130 kan dan wasan mai shekaru 29. (Star)

Dan wasan bayan Manchester United da Ingila Harry Maguire, mai shekara 32, zai iya komawa Saudiyya, inda kungiyoyi kamar Al-Nassr da Al-Ettifaq ke nuna sha’awar daukarsa. (Sunday Mirror)

United na da zabin tsawaita kwantiragin Maguire a Old Trafford har bayan bazara mai zuwa, amma da wuya ta iya yin hakan. (Sunday Express)

Liverpool ta shirya kashe fam miliyan 130 kan dan wasan Bayern Munich da Faransa Michael Olise, mai shekara 23, a kasuwar musayar yan wasan kwallon kafa ta 2026 domin maye gurbin dan kasar Masar, Mohamed Salah mai shekara 33.(Fichajes)

Liverpool ba ta son barin dan wasan baya na Faransa Ibrahima Konate ya tashi a watan Janairu, yayin da Real Madrid ke zawarcinsa, kuma ta ci gaba da dagewa kan ci gaba da rike dan wasan mai shekaru 26 a Anfield na dogon lokaci duk da rashin yin katabus sosai a kakar wasa ta bana. (Football Isider)

Daya daga cikin masu kungiyar Manchester United Sir Jim Ratcliffe ya yi imanin kociyan kungiyar Ruben Amorim ya cancanci ya ci gaba da horar da kungiyar ta Old Trafford. (The I)

Tsohon kocin Barcelona Xavi ya umurci wakilansa da su yi watsi da tayin da kungiyoyin kwallon kafa na Saudiyya suka yi masa, don haka kofarsa a bude take idan har aikin kocin Manchester United ya samu. (Caughtoffside)

Brentford na son biyan Villarreal fam miliyan 26 kan dan wasan gaban Kamaru Etta Eyong, mai shekara 21. (Fichajes)

Barcelona za ta kara yin zawarcin dan wasan bayan Borussia Dortmund da Jamus Nico Schlotterbeck, mai shekara 25, wanda za a iya barin kungiyar a kyauta a bazara mai zuwa. (Sports Spanish)

Bayern Munich ta bayyana golan AC Milan da Faransa Mike Maignan mai shekaru 30 a matsayin wanda zai maye gurbin Manuel Neuer mai shekaru 39 a duniya. (Talk)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 9   +   2   =