Mutuwar shugaban mata (women leaders) Biyar a Karamar Hukumomin Lagos Ya Haifar da Bincike kan zargin ƙungiyar asiri
Gidan jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mutuwar ‘yan siyasa har guda biyar a wasu kananan hukumomi na Jihar Lagos ta jefa al’umma cikin rudani, musamman matan da ke da rinjaye a cikin al’umma. Wannan lamari, wanda ya faru cikin ƙasa da watanni biyu, ya sa mutane da hukumomin yankin suka koma neman taimako daga al’ada, malamai na coci, da limamai.
Lamarin, wanda aka ruwaito a wasu Karamar Hukumomi kamar Somolu, Bariga, da wasu a yankunan mainland da Ikorodu, ya haifar da tsoron cewa akwai asirce-asirce, wanda ya sa aka gaggauta tuntubar masu al’ada, malaman coci da limamai.
Wadanda suka mutu an bayyana su a matsayin mata masu rinjaye a al’ummominsu—shugabannin kasuwa biyu, shugabar kungiyar ci gaban al’umma (CDA), shugabar kungiyar hadin kan mata, da kuma mai kula da yunkurin matasa. Mutuwarsu ta faru tsakanin karshen Satumba da farkon Oktoba 2025, inda aka bayyana dalilin mutuwarsu a matsayin “al’amari mai bantsoro”
A galibi a cikin Karamar Hukumomi masu yawan jama’a kamar Somolu, Bariga, Ikorodu, da Agege, wadanda aka san su da yawan shugabannin al’umma amma kuma a wasu lokuta ana samun rahotannin tashin hankali na asiri.
Masu fashin baƙi akan mutuwar sun bayyana cewa matan sun fadi a lokacin tarurruka ko a gidajensu, ba tare da alamun rashin lafiya ba. Har yanzu ana jiran sakamakon binciken gawarwaki,
Iyalai da mazauna yankin da ke cikin damuwa sun shirya addu’o’in taro da ziyartar gidajen al’ada a Badagry da Jihar Ogun. Wasu LGAs sun dakatar da ayyukan kungiyoyin mata har sai an kammala “tsaftacewa na al’ada.”Malaman coci daga Kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) suna cewa wannan “shiri ne na aljanu,” yayin da masu al’ada ke nuni da rikice-rikicen filaye ko fada a siyasa a matsayin abubuwan da ke jawo lamarin.