Rikicin Korar Ma’aikata: Yadda Dangote ya yi tayin biyan albashin shekaru biyar ba tare da aiki ba ga ma’aikatan da ta kora – Majiyoyi
Matatar mai ta Dangote ta yi tayin biyan albashin ma’aikatan da ta kora na tsawon shekaru biyar ba tare da aikin komai ba, domin kaucewa yiwuwar ɓarna daga hannunsu, amma ƙungiyar ma’aikata ta PENGASSAN ta ƙi amincewa da hakan.
Majiyoyi sun shaida wa Premium Times cewa duk da damuwar gwamnati kan nauyin kuɗin, Dangote ya dage cewa hakan ya fi sauƙi a gare shi fiye da barin ma’aikatan da bai amincewa da su ba a cikin masana’antar.
Sai dai PENGASSAN ta zabi a mayar da ma’aikatan wasu sassan kamfanonin Dangote tare da cikakken albashi, abin da aka amince da shi bayan sulhu da gwamnatin tarayya ta shiga tsakani.
Matatar Dangote ta kori ma’aikatan ne bisa zargin aikata barna da kawo barazana ga tsaro da aikin masana’antar.
Wannan mataki ne da ya tayar da rigima, inda PENGASSAN ta umarci mambobinta su janye ayyuka, kafin daga baya a cimma matsaya ta sulhu.
Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, ya yi gargadi cewa za a koma yajin aiki idan Dangote ya karya yarjejeniyar.