Hukumar Alhazai ta sanar da ranar Ƙarshen biyan rabin kudin kujera

0
5

Hukumar jin dadin alhazai ta Kano ta tabbatar da cewa ranar 8 ga Oktoba, 2025 ne ƙarshe wa’adin biyan kashi 50% na kujerun Hajjin bana.

Shugaban Hukumar Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Alhamis a ofishinsa.

A cewarsa, hukumar Kula Da Alhazai ta Kasa (NAHCON) ce ta bayar da wannan umarni, inda ta wajabta wa kowace jiha ta tura rabin kujerun da aka ware mata kafin ko a ranar 8 ga Oktoba, 2025.

Dambappa ya bukaci masu niyyar zuwa aikin Hajji da su yi gaggawar aiwatar da biyan kuɗinsu cikin lokaci domin ganin jihar Kano ta ci gaba da rike dukkan kujerunta.

Jihar Kano dai ta samu jimillar kujeru 5,684 domin aikin Hajjin shekarar 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 10   +   4   =