Gwamnatin tarayya ta sanya wajibi ga dukkan ɗalibai da suka kammala karatu a Najeriya ko ƙasashen waje su mika aikin binciken karatu (thesis ko project) zuwa ma’ajiyar NERD kafin a ɗauke su ko su shiga shirin NYSC.
Wannan na daga cikin sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da su a karkashin Dokar NYSC, domin hana mika takardun bogi da tabbatar da ingancin takardun karatu.
Sanarwar ta ce daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, babu ɗalibin da za a ɗauka ko ya shiga shirin NYSC ba tare da shaidar bin wannan doka ba.
Sai dai ba ta shafi masu hidima a yanzu ko waɗanda aka riga aka ɗauka kafin wannan rana ba.
A cewar gwamnati, tsarin zai taimaka wajen kare dukiyar ilimin ƙasa, dawo da martaba ga takardun karatu, tare da samar wa ɗalibai da malamai damar samun kuɗaɗen shiga daga binciken da suka mika.