Fiye da ƴan Najeriya miliyan 6.2 ne suka kammala rajistar su ta yanar gizo a shirin ci gaba da rajistar masu zaɓe a mako na shida na aikin, a cewar bayanan da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar a ranar Litinin.
Kididdigar da aka wallafa a shafin X na hukumar da kuma shafinta na yanar gizo ta nuna cewa jimillar 6,232,673 ne suka yi rajista tsakanin 22 zuwa 28 ga Satumba, 2025.
Daga cikin wannan adadi, mata sun kai 3,250,338 (kashi 52.15%), yayin da maza suka kasance 2,982,335 (kashi 47.85%). Matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 34 sun fi rinjaye da adadin 4,230,715. Dalibai sun taka muhimmiyar rawa da 1,565,824, yayin da masu bukata ta mussaman suka kai 137,865.
INEC ta kuma bayyana cewa a mako na biyar (22–26 ga Satumba, 2025), mutane 1,004,132 daga cikin ‘yan Najeriya ne suka kammala rajistarsu ta yanar gizo da ta ofis.
Cikin wannan adadi, 537,743 sun kammala rajistarsu ta yanar gizo, yayin da 466,389 suka kammala ta ofis.