
Shahararren tsohon dan wasan Super Eagles Yakubu Aiyegbeni ya bayyana dalilin da ya sa Najeriya ke samun wahalar zura kwallaye a kodayaushe.
A cewarsa ƙungiyar tana cike da ƴan wasan tsakiya amma masu tsaro maimakon masu taimakawa kai hari.
“Idan muka kalli kungiyar, muna da ‘yan wasan tsakiya masu yawa tarewa da yawa kuma ba ‘yan wasan tsakiya masu kai hari ba,” in ji Yakubu a ranar Lahadi ya fadawa a shirin Oliseh.
“Idan da na taka leda a wannan kungiyar ta yanzu, zan yi fama da rashin zura kwallaye a raga.
“Saboda idan na kalli Osimhen idan yana wasa, yana fada ne saboda ya riga ya san lokacin da ya kamata yaga ya zura kwallaye,” in ji shi.
Kafin ya yi ritaya Yakubu ya ci wa Eagles kwallaye 21 a wasanni 58.




