Tsohon dan wasan Manchester United Paul Scholes ya soki dan wasan gefe na Barcelona Marcus Rashford bayan ya zura kwallaye biyu a ragar Newcastle.
“Ba tare da shakka ba, hazakar Rashford tana da ban mamaki yana nuna ta a manyan wasanni, kamar wasam. Kwalla ta biyu ta haskaka. Amma yana da wahala a gare ni in yi masa murna da gaske, musamman saboda halayensa.
“A Manchester United, lokacin da ya tafi, na dauki yanayin a matsayin abin kunya. Idan kuka samu sabani da kocin- lafiya lau, amma kuna da abokan wasa, magoya bayan 80,000 a filin wasa, kuma dole ne ku yi ƙoƙari. Sau da yawa ina ganin shi yana tafiya kamar bai damu ba … Ina tsammanin ya ci amanar Manchester United yadda ya kamata.
Kuma idan ka ci amana sau daya za ka sake yi.
Scholes ya ce “Na ga alamun irin wannan a Barcelona wani lokacin kawai ba ya son komawa baya ko kuma ya yi aiki a kungiyar. Hakan ba zai dade ba za’a san shi a Barcelona.”
Rashford ya zura kwallaye biyu a wasan farko na rukuni-rukuni na gasar zakarun Turai a waje inda Newcastle (2-1). A wannan bazarar, ya koma Barcelona a matsayin aro na kaka daya tare da zabin siya daga Manchester United. Dan wasan na gaba yana da kwallaye biyu da kuma taimakawa biyu a wasanni ukun da ya buga a kungiyar ta Catalan.