Najeriya ta gabatar da buƙatar neman karɓar baƙuncin gasar wasannin tsalle-tsalle ta Commonwealth Games a 2030.
Gasar da za a yi wa laƙabi da Abuja 2030, za ta zama karo na farko da za a gudanar da ita a nahiyar Afirka tun bayan fara ta kusan shekara 100 – idan Najeriya ta yi nasara.
“Najeriya ta yunƙura a madadin nahiyar baki ɗaya bisa ƙwarin gwiwar cewa wasannin na 2030 za su buɗe sabon babi na damawa da kowa, da damarmaki, da kuma ‘yan’uwantaka,” a cewar wata sanarwa da gwamnatin Najeriya ta fitar a shafukan sada zumunta.
“Ba Abuja kawai muke so a zo ba, muna so Afirka ta zama fagen da ƙasashen Commonwealth za su yi murnar cika shekara 100 tare da kuma ƙarfafa fatan shiga sabon ƙarni mai yalwa.”
Gasar ta Commonwealth Games ta ƙunshi wasannin daban-daban, wadda akan gudanar duk shekara huɗu tsakanin ƙasashe rainon Ingila.