Kasuwar musayen Yan wasan kwallon kafa a wannan Rana

0
90

Tsohon dan wasan Manchester City Julian Alvarez, mai shekara 25, ya na son ya bar Atletico Madrid a bazara mai zuwa inda Liverpool da Barcelona na sha’awar dan wasan kasar Argentina. (Fichajes – in Spanish, external)

Barcelona na son ta kulla yarjejeniya da Manchester United don siyan dan wasan gaba na Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, kan fan miliyan 26 wanda ya yi kasa da fan miliyan 35 wanda shi ne abinda United ke so , (Star, external)

A wani labarin kuma, United ta maida hankali wajan daukar sabon gola a bazara mai zuwa (Sun, external)

Real Madrid ta kalli yadda dan wasan bayan Arsenal William Saliba mai shekara 24, ya yi wasa a karawar da suka yi da Manchester City a ranar Lahadi kuma ta ci gaba, da nuna sha’awar siyan dan wasan na Faransa.(TBR Football, external)

Kyaftin din Crystal Palace kuma dan wasan baya na Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, har yanzu yana son ya koma taka leda a Liverpool a bazara a matsayin dan wasan da ba shi da kwantiragi da wata kungiya bayan da ya kusan kulla yarjejeniya da zakarun firimiya a baya. GiveMeSport, external)

Kyaftin din Ingila Harry Kane, mai shekara 32, zai iya barin Bayern Munich kan kudi fan miliyan 56.7 a bazara mai zuwa sai dai idan ya bayyana aniyarsa ta barin zakarun na Jamus kafin karshen lokacin bazara. Teamtalk, external)

Tottenham na ci gaba da zawarcin dan wasan Manchester City Savinho, mai shekara 21, kuma watakila ta sake kulla yarjejeniya da dan wasan kasar Brazil a watan janairun (Teamtalk, external)

Haka kuma Spurs ta shirya ta yi wa dan wasan Real Sociedad Brais Mendez mai shekara 28 tayin fan miliyan 35 don siyansa a watan Janairu. (Fichajes – in Spanish, external)

Chelsea na son daukar dan wasan Manchester City Nico O’Reilly, ya yin da Leeds United da Bayer Leverkusen da kuma Lyon duk suna zawarcin dan wasan mai shekara 20 (Football Insider, external)

Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 3   +   9   =