Akwai sha’awar dan wasan gaba na Arsenal Gabriel Jesus daga Everton da West Ham United. Yana da sha’awar samun mintuna na wasa na yau da kullun kafin gasar cin kofin duniya, da zarar ya dawo lafiya. (FootballTransfers)
Barcelona za ta kara da Bayern Munich wajen siyan dan wasan baya na Crystal Palace Marc Guéhi a farkon watan Janairu. Liverpool FC ta shirya tsaf domin daukar shi a matsayin kyauta a bazara mai zuwa. (Insider Football)
Getafe na neman daukar’Yan wasan biyu na Real Madrid Raúl Asencio da Gonzalo García a matsayin aro a kasuwar musayar ‘yan wasa ta Janairu. (Fichajes)
Barcelona ba ta ganin yanayin Kwantiragin Ferran Torres a matsayin matsala. Kwantiraginsa na yanzu zai kare ne a shekarar 2027 amma babu gaggawar bude tattaunawa kan karin wa’adi ga Dan wasan. (MARCA)
Sha’awar Real Madrid akan dan wasan tsakiyar Liverpool Alexis Mac Allister gaskiya ne amma ba a sa ran zai kai ga wani abu na zahiri a 2026. Suna da wasu zabuka da suka fifita da farko. (TEAMtalk)
An danganta Chelsea da dan wasan gaba na Athletic Club Maroan Sannadi. Kungiyar ta La Liga ba ta da sha’awar siyar da dan wasan mai shekaru 24 a watan Janairu. (Foot Africa)
Manchester City ta nemi Bruno Guimarães a wannan bazarar. Amma Amsar Newcastle United ta kasance cikin sauri ‘a’a bana sayarwa bane. (Graeme Bailey)
Aston Villa da Newcastle United duka suna zawarcin dan wasan Borussia Dortmund Julian Brandt. Za a iya daukar sa a matsayin kyauta a karshen kakar wasa ta bana amma kuma mai yuwuwa kungiyar ta masa farashi mai rahusa a watan Janairu. (CaughtOffside)
Everton ta shirya tsaf domin hana Manchester United cigaba da zawarcin Jarrad Branthwaite. (Insider Football)
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea tana sa ido kan yadda dan wasan Manchester City Nico O’Reilly ke samun ci gaba. Leeds United da Bayer Leverkusen da kuma Lyon suma suna sha’awar dan wasan mai shekara 20. (Insider Football)
Babban Dan wasan da Real Madrid zata yi zawarcinsa a kasuwar saye da sayar wa da ‘yan wasa ta bazara mai zuwa shine Michael Olise daga Bayern Munich. (Alan Nixon)
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Aston Villa Monchi na shirin barin kulob din. Villa ta fara rashin nasara a kakar wasa ta bana a karkashin kocinta Unai Emery, inda ta zura kwallo daya kacal a wasanni biyar na gasar Premier league. (The Athletic FC)
Wanna gyara ya kamata kungiyar ku ta yi?