Kamfanin Retail Supermarkets Nigeria Limited (RSNL), mamallakin ShopRite a Najeriya, ya tabbatar da cewa zai ci gaba da gudanar da kasuwanci a ƙasar, duk da jita-jitar da ke yawo cewa zai iya rufewa.
Rahoton Daily Trust ya nuna yadda shagunan suka fara yin fanko, abin da ya sa ake ganin suna dab da fita daga kasuwa.
Sai dai kamfanin, wanda sabbin masu zuba jari suka karfafa, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa yana aiwatar da sabon tsarin kasuwanci domin dacewa da halin tattalin arzikin Najeriya.
Sanarwar ta ce: “Tsarin kasuwancin da muka gada lokacin sayen kamfanin ya dogara ne da manyan shaguna, shigo da kaya daga ƙasashen waje, da kuma tsadar kula da harkoki. Amma wannan tsarin bai dace da halin tattalin arzikin Najeriya na yanzu ba, inda ake fama da sauyin kudin canji, tashin farashin kaya da ƙarancin kuɗi.”
Kamfanin ya bayyana cewa sabon tsarin zai rage dogaro da shigo da kaya daga waje, inda ya ce sama da kashi 80 cikin 100 na kayayyakin da ake sayarwa yanzu daga cikin gida ake samo su.
Haka kuma ya ce wannan sabon tsarin zai taimaka wajen daidaita harkoki da kuma sake farfado da kasuwancin domin ci gaba a dogon lokaci.
Shugabar dabarun kasuwancin kamfanin, Bunmi Adeleye, ta bayyana wannan mataki a matsayin sabon ginin da zai maida ShopRite ya zama na cikin gida sosai.