Kamfanin matatar mai ta Dangote zai fara shirin jigilar man fetur kyauta daga ranar Litinin mai zuwa, daga rahoton jaridar Punch.
Mai magana da yawun rukunin kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya bayyana a cikin sanarwar cewa shirin zai fara ne daga jihohin Kudu maso Yamma, Kwara, Delta, Rivers da Edo tare da babban birnin tarayya Abuja
Ya kara da cewa matatar man ta riga ta rage farashin man fetur zuwa Naira 841 a kowace lita a Lagos da sauran jihohin Kudu maso yamma, yayin da a Abuja, Edo, Kwara, Rivers da Delta za a sayar da shi kan Naira 851 a kowace lita.
A baya dai an shirya fara wannan shiri tun watan Agusta, amma aka samu tsaiko saboda matsalolin sufuri daga kasar China.
Rahotanni sun ce an riga an samu motocin dakon mai sama da 1,000 da za su fara aikin rabon man fetur ɗin, kuma ana sa ran karin jihohi za su shiga cikin shirin nan gaba kadan yayin da karin manyan motocin kamfanin ke iso wa Najeriya.
A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, kamfanin Dangote ya ce ya kaddamar da motoci 10,000 masu amfani da iskar gas (CNG) domin karfafa jigilar kayayyaki da rage kudin safara a fadin kasar.