Ƙungiyar direbobin dakon mai ta Nijeriya (NUPENG) ta janye shirin shiga yajin aiki bayan ta cimma yarjejeniya da shugabannin matatar mai ta Dangote kan batun ‘yancin ma’aikata na shiga ƙungiyoyin ƙwadago.
An cimma wannan yarjejeniya ne a wani taro na sirri da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta jagoranta, tare da halartar Ministan Kuɗi da wakilan ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya (NLC).
Muƙaddashin sakataren yaɗa labarai na NLC, Benson Upah, ya tabbatar da sakamakon tattaunawar, yayin da ma’aikatar ƙwadagon tarayya ta bayyana cewa za ta fitar da sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba.
An tabbatar da cewa shiga ƙungiyar ƙwadago haƙƙi ne da doka ta tanada.
Ma’aikatan matatar Dangote za su fara samun damar shiga ƙungiya nan take, kuma za a kammala tsarin cikin mako biyu.
An tabbatar da cewa babu ma’aikacin da za a ci zarafinsa ko a hukunta shi saboda sha’awar shiga ƙungiyar ƙwadago.
Sakamakon haka, NUPENG ta sanar da dakatar da shirin yajin aikin nata nan take. An kuma tsara cewa za a sanar da Ministan Ƙwadago halin da ake ciki mako guda bayan an kammala aiwatar da tsarin.
Ƙungiyar NUPENG ta yi barazanar shiga yajin aiki ne bayan ta zargi kamfanin matatar Dangote da kin amincewa da ‘yancin ma’aikatansa na shiga ƙungiyoyin ƙwadago, abin da ya haifar da damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki kan batutuwan ƙwadago a Nijeriya.