Ƙofar Zamfara a buɗe take ga masu zuba jari

0
8

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar sauya labarin jihar daga matsaloli zuwa dama mai fa’ida ta fuskar tattalin arziƙi da hannun jari.

A jawabinsa ga masu zuba jari a taron AfSNET na biyar da aka gudanar a ranar Asabar a birnin Algiers, Aljeriya, Gwamna Lawal ya ce:

“Ƙofa a buɗe take ga masu sha’awar zuba jari. Zamfara tana da arzikin ƙasa mai yawa wanda bai taɓa samun cikakken amfani ba.”

Ya yi nuni da cewa, ban da zinariya, jihar na da tagulla, lithium, tantalite, da granite – albarkatun da ke iya jawo hankalin manyan masu saka jari daga gida da waje.

Lawal ya kuma bayyana cewa Zamfara tana shirye-shiryen kulla yarjejeniyoyin saka jari kamar irin wanda jihar Cross River ta cimma da Afreximbank, tare da burin samun haɗin gwiwar gaggawa da zai baiwa jihar damar amfana daga irin waɗannan manyan dama da tallafin gwamnatin tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   7   =