Taƙaitattun Labarai tare da Munamafricanews

0
107
  • Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta kai ɗauki kan waɗanda ambaliyar ta shafa a wasu garuruwan jihar Kaduna, inda ta samu nasarar ceto wasu waɗanda ambaliyar ta rutsa da su.
  • Hukumomi a Isra’ila sun ce wani jirgi maras matuƙi da aka aika daga Yemen ya kai hari kan filin jirgin sama na Ramon Airport a kudancin ƙasar.
  • Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Magajin-Wando da ke karamar hukumar Dandume.
  • Firaministan ƙasar Japan Shigeru Ishiba ya yanke shawarar yin murabus a yau lahadi, inda ‘yan jam’iyyarsa suka yi kira da a kawo sauyi a harkokin shugabanci biyo bayan rashin kyakkyawan sakamakon da aka samu a zaben ‘yan majalisar dattawan ƙasar da aka gudanar a wannan bazarar.
  • A Najeriya ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaron farin kaya da ake kira Civil Defence 8, kana suka yi awon gaba da wasu ma’aikata ‘yan ƙasar China a jihar  Edo da ke kudu maso kudancin ƙasar, kamar yadda kakakin Civil Defence ɗin ya bayyana.
  • Rasha ta kai harin sama mafi girma a Ukraine tun bayan da aka fara yaƙi tsakanin ƙasashen biyu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane huɗu, baya ga lalata gine-ginen gwamnati, harin da shugaba Volodymyr Zelensky ya ce zai iya tsawaita yaƙin.
  • A Jamhuriyar Nijar, shirin wayar da kan jama’a na shekarar 2025 kan iya karatu ya kai ga mutum 24,573, ciki har da mata 19,619, inda aka gwada mutum 18,741 a cikinsu kuma aka tabbatar da cewa mutum 13,132 sun iya karatu, a cewar hukumomin kasar.
  • Mazauna Dar-El-Jamal na Jihar Borno sun ce an kai harin ne da maraice, inda gomman ‘yan ta’adda na Boko Haram suka isa garin a kan babura suna harbe-harbe da kuma ƙona gidaje.
  • Dakarun Isra’ila sun yi amfani da ƙarfi wajen kai hari tare da musguna wa mata Falasɗinawa da ke zanga-zanga a Umm al Fahm, kan yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza.
  • Dan wasan tsakiya na Manchester United Bruno Fernandes, mai shekara 30, ya yi watsi da tayin da wasu kungiyoyin uku na Saudiyya suka yi masa a wannan bazara, inda dan wasan kasar Portugal ya zabi ci gaba da zama a Old Trafford. Sai dai kyaftin din United bai dakatar da tattaunawa da Saudiyya ba saboda wakilan kungiyoyin har yanzu suna da niyyar siyan shi a kaka mai zuwa.
  • Bayern Munich na tunanin ko ta dauko dan wasan gefe na Liverpool Cody Gakpo a lokacin bazara. Dan wasan kasar Netherlands na cikin ‘yan wasa masu kai hari da kungiyar ta Jamus ke sha’awa, wadda ta dauki tsohon abokin wasansa Luis Diaz.
  • Chelsea ta samu tayin fam miliyan 59.5 daga kungiyar Al-Qadsiah ta Saudi Pro league kan dan wasan tsakiya na Brazil Andrey Santos. Dan wasan mai shekara 21 ya shafe kakar wasa ta bara a matsayin aro Strasbourg da ke Faransa.
  • Morgan Rogers ya fito a matsayin dan wasan da Tottenham ke son daukowa a watan Janairu. Kocin Spurs Thomas Frank yana goyon bayan dan wasan tsakiyar Aston Villa, mai shekara 23, wanda a halin yanzu yake taka leda a tawagar kwallon kafa ta Ingila.
  • Juventus na son daukar dan wasan tsakiyar Real Madrid, Dani Cebellos a watan Janairu. Tun a bazara ne kungiyar ta kasar Italiya ke zawarcin dan wasan kasar Sfaniya, mai shekara 29 amma ba su cimma matsaya ba.
  • Arsenal ba ta anniyar barin dan wasan Belgium Leandro Trossard ficewa daga kungiyar. An danganta dan wasan mai shekaru 30 da komawa Besiktas amma ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar ta Arsenal a watan da ya gabata.
  • Dan wasan bayan Liverpool Giovanni Leoni, mai shekara 18, ya ki amincewa da komawa Newcastle a lokacin da yake Parma duk da cewa Magpies ta nuna cewa za ta ba kungiyar ta Italiya kudi fiye da na Liverpool don siyan shi.
  • Tsohon dan wasan Liverpool da Bayern Munich da Sfaniya Thiago Alcantara mai shekara 34, ya amince ya sake komawa Barcelona a matsayin daya daga cikin masu taimakawa kocin kungiyar Hansi Flick.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 3   +   1   =