~Gwamnan jihar Neja Umar Bago ya sauke kwamishinoninsa da wasu masu riƙe da muƙamai daban-daban, inda ya ce yayin da wasu daga cikin su ba su taɓuka abin kirki ba, wasu kuma za su fi dacewa a wasu ma’aikatun na daban.
~Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi gargadin yajin aiki mai tsanani saboda rashin cika yarjejeniyar shekarar 2009, wanda ya hada da batutuwan kudade. Wannan na iya kawo cikas ga ilimi a jami’o’i idan tattaunawa ta gaza.
~Hukumar NAFDAC ta gargadi jama’a game da jabun allurar Gold Vision Oxytocin da lambar rajista ta karya, tana kira da a guji amfani da ita don gujewa haɗari game da lafiya.
~Qatar Ta Yi Alkawarin Zuba Jarin $103 Biliyan a Afirka don bunkasatattalinarziƙin nahiyar
~Mutane 13 sun yayin tserewa harin yan’bindiga ya yankin tafkin cadi.
~‘Yan tawayen M23 da Rwanda ke goyon baya, sun ƙara mamaye ƙarin yankuna a gabashin Jamhuriyar Kwango, ciki har da wasu sassa yankin Goma, wanda ke haifar da fargabar rikici a yankin.
~A kalla mutum 11 sun mutu bayan guguwar Chido ta lalata yankin Faransa na Mayotte, wanda ke cikin tekun Indiya, Inda guguwar ta haifar da ɓarna mai yawa.
~Jiragen ruwa sama da 50 daga kasashe 44, ciki har da Afirka ta Kudu da Kenya, sun kaiwa yankin gaza.
~Wike ya sake nanata goyon bayansa ga Shugaba Tinubu, inda ya ce fafatawa da shi a zaɓe tamkar rashin girmamawa ne ga shugaban.
~Gwamnatin Nijeriya ta ce shiyyar arewa maso yammacin ƙasar ce ke da kaso mafi yawa na kuɗaɗen da aka ware wa manyan ayyukan gwamnatin tarayya, inda aka amince wa shiyyar kusan naira triliyan 6, kwatankwacin kashi 40 na duka kuɗaɗen da aka ware don gudanar da ayukka.
~Gamayyar ƙwararru ta IAGS da ke nazartar laifukan kisan ƙare dangi na ƙasa da ƙasa sun bayyana abin da Isra’ila ke aikatawa a Gaza a matsayin kisan ƙare dangi bayan da suka ce ta kai dukkanin matakan da ya kamata a bayyana ayyukanta da kisan ƙare dangin ƙarƙashin dokokin 1948, matakin da ke zuwa a dai dai lokacin da Isra’ilan ke ci gaba da faɗaɗa hare-hare a sassan Gazan.
~Shugaban Xi Jinping na China na karɓar baƙuncin shugabannin ƙasashe sama da 20, ciki harda Vladimir Putin Rasha da Narendra Modi India, a wani taro da babbar manufarsa ita ce tabbatar da China a matsayin jagora don kare muradunsu.
~Ana ci gaba da aikin ceto don lalubo masu sauran lumfashi a ɓaraguzan gine-gine bayan ƙaƙƙarfar girgizar ƙasar Afghanistan ta kashe mutane fiye da 800 baya jikkata wasu dubbai, kodayake matsalar rashin kyawun hanya da katsewar sadarwa ta haddasa gagarumin naƙasu a ƙoƙarin naceto rayuka.
~Taƙaddama ta kaure tsakanin Mai bai wa shugaban ƙasa shawara a kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu da tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasir El Rufai akan zargin biyan ƴan ta’adda domin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.
~Alƙaluma daga shafin da ke bibiyar hada-hadar sauyin sheƙar ‘yan wasanni na FootballTransfers.com, sun nuna cewar jimillar ƙungiyoyin da ke gasar Firimiyar Ingila, sun kakshe Fam Biliyan 2 da miliyan 600 wajen sayen ‘yan wasa.
~Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gana da takwaransa na Iran Masoud Pezeshkian a gefen taron kungiyar SCO a birnin Tianjin na kasar China.
~Wata likita ta yi nasarar cire harsashi daga jikin wata yarinya Bafalasdiniya bayan dakarun Isra’ila sun harbe ta a gadon baya a harin da suka kai Gaza.
~Ana sa ran matakin na 5G zai karfafa hanyoyin sadarwa na kasar, da bayar da damar hanzarta aika bayanai da karfafa hanyoyin sadarwa.