Newcastle United a shirye suke su bari ɗan wasansu, Alexander Isak ɗan ƙasar Sweden mai shekaru 25, ya koma Liverpool, amma sai idan Reds ɗin sun biya kuɗin tarihin cinikin ‘yan wasa a Birtaniya, wanda ya kai fam miliyan 130.
Aston Villa sun yi tattaunawa da Manchester United kan yiwuwar sayen ɗan wasan Ingila, Jadon Sancho, mai shekaru 25.
Haka kuma, Aston Villa sun nuna sha’awar sayen mai tsaron gida ɗan ƙasar Belgium, Senne Lammens, mai shekaru 23, daga ƙungiyar Royal Antwerp.
Bayern Munich sun janye tayinsu na sayen ɗan wasan gaba na Chelsea kuma ɗan ƙasar Senegal, Nicolas Jackson, mai shekaru 24.
Tottenham sun tunkari Atalanta game da yiwuwar sayen ɗan wasan gaba na Najeriya, Ademola Lookman, amma suna fuskantar gasa daga Bayern Munich kan ɗan wasan mai shekaru 27.
Galatasaray suna tattaunawa da Tottenham don siyan ɗan wasan tsakiya ɗan ƙasar Mali, Yves Bissouma, mai shekaru 29.
Mun Aje Muku Link na WhatsApp a comment Adaure ashiga mungode
AC Milan sun yi tayi na hukuma don sayen ɗan wasan tsakiya na Ingila, Joe Gomez, mai shekaru 28, daga Liverpool, kuma a yanzu ƙungiyoyin suna tattaunawa kan yarjejeniyar.
Fenerbahce suna ƙoƙarin siyan mai tsaron gida ɗan Brazil, Ederson, mai shekaru 32, daga Manchester City, bayan da abokan hamayyarsu ta Turkiyya, Galatasaray suka yi tayin Euro miliyan 10 (£8.7m) wanda aka ƙi.
Newcastle United suna son sayen ɗan wasan gaba ɗan ƙasar Ukraine, Artem Dovbyk, mai shekaru 28, daga Roma, wanda ake kimanta darajarsa da fam miliyan 30, a matsayin aro wanda za su saye shi gabaɗaya nan gaba.
Aston Villa sun cimma yarjejeniya da Aberdeen don sayen matashin ɗan wasan tsakiya ɗan ƙasar Scotland mai shekaru 17, Fletcher Boyd.
Ku Duba comment Mun Aje Muku Link adaure ayi following share like comment mungode
Aston Villa, ƙungiyar Unai Emery, suna dab da kammala sayen ɗanE bayan Sweden mai shekaru 31, Victor Lindelof, wanda yake kyauta bayan ya bar Manchester United a ƙarshen kwantiraginsa.