LabaraiNajeriyaSiyasa

Ganduje shugaba ne da ba ya aikata cin-hanci da rashawa – Muhammad Garba

Muhammad Garba, babban hadimin tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya karyata zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa jagoransa.

Ya bayyana wannan zargi a matsayin yarfe na siyasa don rudar da jama’a.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, Garba, wanda tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai ne a jihar, ya ce ba gaskiya ba ne cewa Ganduje ɗan siyasa ne mai cin hanci kamar yadda magajinsa ya yi ikirari.

A cewarsa, Ganduje ya shugabanci jihar cikin gaskiya, amana, da bin ƙa’ida tare da aiwatar da manyan ayyuka a lokacin mulkinsa na shekaru takwas.

Garba ya nuna damuwa kan abin da ya kira “ƙoƙarin gwamnatin jihar Kano na gangan wajen danganta Ganduje da karkatar da kuɗi, rashawa, da aikata ba daidai ba da ta ke yi,” musamman kan zarge-zargen kashe kuɗi fiye da ƙima ta ofishin ‘Protocol’ da kuma mallakar ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.

A cewarsa, Ganduje ya ba da muhimmanci ga ci gaban jihar da kuma sarrafa dukiyar gwamnati yadda ya kamata a lokacin da ya ke kan mulki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Prove your humanity: 3   +   3   =  

Back to top button