LabaraiNajeriya

Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Gombe ta ja hankalin matasa kan gaggawar yaɗa labarai marasa tushe

Wannan gargaɗi na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP. Buhari Abdullahi, ya fitar ta a ranar Talata.

Sanarwar ta fayyace gaskiya dagane da wani lamarin daya faru a ranar Litinin da misalin ƙarfe 10:30 na dare a kan titin Unguwar Malam Inna, tsakanin ƴansanda masu sintiri wato (Patrol 999) da wani matsahi mai babur.

Buhari ya bayyana cewa, ya ziyarci matsayin mai suna, Rabiu Giɗaɗo, a asibiti mallakar gwamnatin tarayya a jihar Gombe (FTH), ya na mai cewa sun tattaunawa kan gaskiyar abin da ya faru.

A safiyar ranar Talata ne dai hotunan matashin ɗauke da raunuka suka karaɗe shafukan sada zumunta, tare da cewa ƴansanda ne suka buge shi akan hanyar su ta zuwa asibiti tare da matarsa mai juna biyu.

Sai dai DSP. Buhari ya ce, matashin ya tabbatar masa cewa, shi kaɗai ne akan babur ɗin ba tare da wata mace mai ciki da zai kai asibiti ba, kuma bai san abin da ya ji masa ciwo ba, saɓanin abin da ake yaɗa wa.

“Ya shaida min cewar ya ga ƴansanda, amma bai tsaya ba. Matsahin ya tabbatar min da cewa ya faɗi da babur ɗinsa ne kuma yanzu haka babur ɗin ya na wajen gyara.

Rundunar ta ce, ta ƙadamar da binciken ƙwa-ƙwaf kan lamarin, biyo bayan ƙiraye-ƙirayen da ta samu domin ɗaukar matakan da suka dace.

“Muna ƙira ga jama’a da su guji yaɗa jita-jita, wato labari da ba shi da tushe. Zamu bibiya gami da ɗaukar mataki akan dukkan wanda muka samu da hannu wajen yaɗa labarin ƙarya a kan wannan lamarin,” in ji Buhari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Prove your humanity: 5   +   4   =  

Back to top button