
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da kwace iko da wuraren hakar zinarenta daga kamfanin kasar Australia.
Sojojin sun zargi kamfanin kasar Australia da ke gudanar da aikin hakar zinaren da “saba ka’ida” a yayin da suke neman samun cikakken iko kan albarkatun kasarsu.
Gwamnatin sojin da ke jagorantar kasar ta yammacin Afirka tun bayan juyin mulkin 2023, ta na yin da’awar magance matsalolin tsaro daban-daban da Nijar ke fuskanta.
Kamfanin Australia mai suna McKinel Resources Limited da ke aikin hakar zinaren ya fara aiki ne a Nijar a shekarar 2019 bayan ya sayi kaso mafi tsoka na hannun jari daga wani kamfanin gwamnati.




