Yan’bindiga sun dauke mutane 50 tare da kashe mutane 6 a jihar Katsina.

0
106

Ƴanbindiga Sun Kwashi Mutane Sama da 50, Sun Kashe 6 a Jihar KatsinaMazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta jihar Katsina sun ce ƴanbindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi mutane sama da 50, da suka hada da mata da ƙananan yara.

Maharan sun kashe akalla mutum 6, inda suka sake kai wani hari a yankin karamar hukumar Dandume ta jihar.Malam Ya’u Ciɓauna, mazaunin garin Layin Garaa na ƙaramar hukumar Funtua, ya ce: “Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ƴanmata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53.

Sun kashe mutum 2 a Layin Garaa na ƙaramar hukumar Funtua da kuma wasu mutum 4 garin Mai Kwama a cikin ƙaramar hukumar Dandume.”Maigarin Layin Garaa, Mustapha Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mutanen sa na cikin mawuyacin hali na rashin abinci, kwatsam kuma sai ga wannan matsala ta harin ƴanbindiga.

Hukumar ƴansanda a jihar Katsina ta ce tana kan bincike a kai lamarin, domin haka ba za ta ce komai ba sai ta kammala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   4   =